Sakon Sonic Man: Dan An Yaudari Saurayi Ko Budurwa Ba Zai Zama Karshen Rayuwa Ba

Sonic Man

Muna fuskantar kalubale da dama mussamam ma daga wajen ‘yan kasuwa na rashin samun maslaha yadda zasu sayar da fayafayenmu inji Sonic man.

Sani Suleman wand aka fi sani da Sonic Man, dai mawakin soyayya ne da ya shafe fiye da shekaru goma yana waka, kamar kowa ya ce ya fara waka ne sakamakon sha’awar isar da sako ta hanyar waka.

Matashi ya ce yana isar da sakonni na musamman kan yaudarar da ‘yan mata ke yiwa samarinsu kokuma akasin hakan, inda yake cewa a wannan lokacin ire-iren wakokin da yake yi kan kwantar da hankalin matasa tare da nunawa matasan cewar don an yaudari saurayi ko budurwa rayuwa zata ci gaba.

Daga karshe ya kara da cewa har yanzu ‘yan kasuwa basu san yadda ya kamata su sayar da ire-irin wakokinsu ba saboda a cewar sa da dama idan masoyansu suka je neman wakokinsu sai ‘yan kasuwan su ce basu da su.

Your browser doesn’t support HTML5

Sakon Sonic Man: Dan An Yaudari Saurayi Ko Budurwa Ba Zai Zama Karshen Rayuwa Ba