Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sana'a Goma Da Goma Ga Editin Ga Harkar Barkwanci : Ali ArtWork


 Ali mohd Idris , Ali ArtWork
Ali mohd Idris , Ali ArtWork

Yau dandali ya sami bakunci edita Ali mohd Idris, wanda aka fi sani da 'Ali artwork, kuma mun zanta da shi ne akan sabuwar sana’arsa wato comedy (barkwanci ) da yake yi a minti daya.

Artwork, ya ce ya fara barkwanci ne bayan ya lura a arewacin Najeriya ba a da masu barkwanci kamar su basketmouth, ko Bovi, da sauransu wanda a cewarsa na daga cikin muhimmaman abubuwan da suka sa ya fara, bayan ya lura yana yawan sa mutane dariya.

Artwork ya bayyana cewa baya ga barkwancin minti guda guda da yake sakawa ta shafukan sadarwa, yakan yi abin nan da turawa kan cewa ‘standup comedy’ wato baiwa mutane nishadi a wuraren nishadi.

Kuma babban burinsa a rayuwa bai wuce yayi fice kamar yadda sauran wadanda ke faggen nishadi suka yi suna da fice ba.

Domin Karin bayani saurari cikakkiyar hirar a nan

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:53 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG