Sabon Fin Din Mission Impossible 6 Ya Mamaye Zukatan Masoya Fim A Daukacin Indiya

Tom Cruise a 'Mission: Impossible – Fallout'.

Kamar yadda aka saba ganin yawancin kasashen duniya kowa na alfarin kallon fina finan al’adun su, yanzu zamani ya sauya kamar yadda masu iya magana suka ce, idan kida ya canza wajibi ne rawa ta canza.

Fina Finan Hollywood sun sami karbuwa a kasar India, inda a yau 27 ga watan yuli ne aka fitar da sabon fin din Mission Impossible 6 na Shaharrren dan wasan Amurka Tom Cruise.

Fim din dai ya zarce kowanne a kasar Indiya, inda ya bar manyan fina-finai irin su, Saheb Biwi Aur Gangster 3 da Nawabzaade wadanda suma yau aka sake su.

Bisa ga nazarin masanin harkokin kasuwanci Taran Adarsha, MI6 ya mamaye kasuwar fina finai a kasar, haka kuma wannan fim ya dawo da martabar Tom a matsayin tauraron taurari.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabon Fin Din Mission Impossible 6 Ya Mamaye Zukatan Masoya Fim A Daukaci Indiya