Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana'antar Hollywood Ka Iya Daukakawa Ko Dakushe Jarumi


Masana’antar shirya fina finai ta Hollywood wuri ne da ka iya daukaka sana’ar mutum ko dukushe ta a cikin minti kalilan. Jarumai 33 sun bace daga wannan masana’antar ba a jin duriyarsu. Amma abin takaici ne idan daya daga cikin jarumai ya bace ba’a ganin sa ko ita ba tare da wani dalili ba.

Duk da cewa hakan na iya kasancewa idan dan fim ya yanke hukuncin yin murabus daga sana’ar fim, wani lokaci yakan faru ne idan masana’antar tayi shawarar cewa ta gama da jarumi, wato bashi da wani amfani kuma. A Hollywood kuskure daya ka iya jefa jarumi cikin ramin da ba zai iya fitowa daga ciki ba, ya sa mutum cikin jerin waddanda ba a bukata kuma.

Haka kuma wani lokacin ba laifin jarumin ko jarumar bane, lamarin sai ya fi lalacewa idan mutum yana rayuwa kazantaciya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG