Rigiji-Gabji "Sahun Giwa Ya Take Na Rakumi"

A dai-dai lokacin da wasu jirge masu sarrafa kansa na Drones, su kaita shawagi a farfajiyar tashar jiragen sama na Gatwick, a kasar Ingila, mahukuntan tashar jirgin sun hana sauka da tashin duk wani jirgi.

A kasar Ingila da Amurka karya dokane mutun ya tura jirgin nasa na drone sararrin samaniya, da ya wuce nisan tsawon gidan bene mai hawa 10, ko kuma mutun ya sake shi a yankunan da jiragen sama ke shawagi, babban laifine.

Duk wanda aka samu da wannan laifin ana iya hukunta shi, har ma yakan iya zuwa gidan kasu na tsawon shekaru 5. Abune mai wuyar sha’ani ace za’a hana shawagin jiragen a yankunan da jiragen sama ke kai komo, a cewar mahukuntan kasar.

Tun da yammacin ranar Laraba gungun wasu jiragen masu sarrafa kansu, keta shawagi a harabar tashar jirgin, wanda ya tilastawa mahukuntan tashar dakatar da duk wasu kaiwa da kawowar jiragen sama, wanda suke ganin hakan na iya shafar harkar tsaro na tashar.

A ‘yan shekarun nan karuwar yawaitar jiragen ya hauhawa, akwai mutane da dama da basu da masaniya, ko makamar sarrafa jirgin ta hanyoyi da suka dace. Yawaitar jirgin yasa jirgin bashi da tsada, kudin shi kan fara da ga dalar Amurka $100 kwatankwacin naira N36,000.

Taswirar Tashar Gatwick

A wani rahoto da ke cewa, a Ingila cikin wannan shekarar an rufe tsashoshin jirage sau 120, a shekarar da ta gabata kuwa an rufe tashoshi sau 93, inda a shekarar 2014 aka samu rahoton rufewar tashoshin sau shida.