Pillars Da Kwara United Sun Yi Rashin Nasara A Gasar Firimiyar Najeriya

Kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers ta dawo fagen fama a gasar zakarun kungiyoyin kwallon kafa ta Najeriya, yayin da suka doke Kano Pillars da ci 1-0 a wasan mako na 11 da aka sakewa lokaci, wanda aka buga a filin wasa na Nnamdi Azikiwe da ke Enugu.

A daya wasan da aka sake bugawa na NPFL mako na 13, Enyimba FC ta ci gaba da taka rawar gani bayan da ta samu nasara 2-0 a kan Kwara United da ta kai mata ziyar har gida.

A farkon wasan duka kungiyoyin sun samar da yanayi da zai bada damar zura kwallaye, kuma a gefe guda, dan wasa Israel Abia wanda ya nemi zura kwallo amma mai tsaron gida na Pillars Joshua Enaholo, bai bashi dama ba.

Zagaye na biyu na wasan shima ya fara kamar zagaye na farko tare da bangarorin biyu suka kasa yin amfani da damar jefa kwallaye da suka samu.