Manchester United: Sai Mun Saye Dan Wasa Jadon Sancho

Cikin yunkurinta na ganin ta inganta 'yan wasanta domin tunkarar wasannin kakar badi.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana shiri domin sayen dan wasan gefe na kungiyar Borussia Dortmund, mai suna Jadon Sancho, dan kasar Ingila mai shekaru 19, da haihuwa.

Kungiyar zata kashe zunzurutun kudi fiye da fam miliyan £100 na kasar Ingila domin dauko dan wasan da zaran an bude hada hadar saye da sayarwa.

Har ila yau Manchester United tana zawarcin dan wasan Benfica, Joao Felix, dan shekaru 19 da haihuwa wanda ake alakanta shi da Real Madrid.

Bayan haka kungiyar ta Manchester itace kungiya ta farko da ta nuna sha'awarta kan dauko dan wasan tsakiya na Leicester City, Youri Tielemans, dan shekaru 21, a duniya wanda yake zaman aro a kungiyar daga Monaco.