Man City Ta Fara Sharar Fage Da Arsenal

Bernardo Silva da Raheem Sterling.

Masu sharhi a fagen wasan kwallon kafa sun yi tsokacin cewa, yanzu Emery zai fahimci irin kalubalen da ke gabansa a gasar ta Premier.

Manchester City ta fara sharar fagen kare kofin gasar Premier da ta lashe a kakar wasannin bara, bayan da ta bi Arsenal har gida ta doke ta da ci 2-0.

Dan wasan City Raheem Sterling ne ya fara zira kwallon farko a minti na 14 a zagayen farko, bayan da ya yi wasan kura da wasu 'yan wasan Arsenal biyu.

Sterling dan wasa ne da ya sha fama da suka a 'yan kwanakin baya saboda rashin kwallaye da ba ya zirawa, musamman ga kasar ta Ingila.

Kwallo ta biyu ta fito ne daga kafar Bernardo Silva bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Shekaru biyu yanzu suka ragewa Sterling a City kafin kwantiraginsa ya kare, kuma kocinsa Pep Guardiola na ta kokarin ya shawo kansa kan bukatar da ya mikawa kungiyar ta neman a kara mai albashinsa.

A daya bangaren kuma, wannan wasa shi ne fitar farko ta sabon kocin Arsenal, Unai Emery, wanda ya maye gurbin Arsene Wenger a watan Mayu.

Masu sharhi a fagen wasan kwallon kafa sun yi tsokacin cewa, yanzu Emery zai fahimci irin kalubalen da ke gabansa a gasar ta Premier.

A baya ya yi ta kurarin cewa za su fara wasansu da kafar dama.