Lokacin Yi da Matasan Najeriya a Gwamnatance Yayi

Manyan gobe

Ana dai cigaba da kira ga matasa da su kasance masu koyi da mazan jiya, su sani fa su ne manyan gobe, su guji duk wani abu da zai bata musu suna tun daga yarintar su. Hon. Nasiru Adhama, yayi wannan kiran inda yake kira da cewar matasa su zama masu kishin kansu da kasa, ganin yadda suka bada hadin kai a zaben da yagabata na shugaban kasa, to lallai yakama ta su cigaba da irin wannan halin.

Don ta bada hadin kai ne kawai gwamnati zata san menene bukatun su idan sun zama masu kishin cigaban kansu. Yace lallai matasa su kasance masu murna da wannan gwamnatin mai zuwa don idan aka duba yadda zababen shugaban kasa ke cewar gwamnatin shi zata maida hankali ne akan matasa, kasan cewar su ke da mafi yawan kaso a yawan kasar don matasa ke da kashi 60 bisa 100.

Ashe kuwa yakamata matasa kada su bari ayi amfani da su wajen tarzoma kowace iri ce. Ya kuma kamata suyi karatun ta natsu, su sani fa duk wasu ‘yan siyasa da zasu sasu yin wani abu na tada zaune tsaye to su sani wadannan ‘yan siyasan ‘yayansu basu wadannan kasar, mafi akasari ‘yayansu na kasashen waje.

Kuma ‘yan mata ma su sani cewar wannan wata damace da zasu nuna bajintar su, don a wasu lokkuta mata sukan yi rawar da tafi ma ta maza. Bisa haka yakamata suma su maida hankali wajen komawa makaranta da samun sana’ar da zata taimaka wajen cigaban kasa baki daya.