Mai Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, Vichai Srivaddhanaprabha tare da ma'aiktansa guda biyu sun rasa rayukansu a wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya auku.
Daga cikin wadanda suka halaka har da matukin jirgin da wani fasinja guda.
Hatsarin ya faru ne a ranar Asabar a yayin da jirgin matukin ya kasa shawo kan jirgin bayan ya kwace masa a lokacin da yake kokarin sauka a wajan filin wasa na King Power, da yammaci don zuwa kallon wasan da kungiyarsa ta Leicester City ta yi da abokiyar karwarta Westham a gasar firimiya lig na bana mako na 10 inda aka tashi kunnen doki 1-1.
Jami'an 'yan sanda na garin Leicester City sun ba da tabbacin aukuwar hatsarin inda suka ce hamshakin mai kudin ya mutu a wannan hatsarin tare da wasu mutane biyu da suka hada da Mr. Nursara Suknamai, da Kaveporn Punpare sai kuma matukin jirgin maisuna Eric Swaffer, da Izabela Roza Lechowicz.
Ku Duba Wannan Ma Yadda Ta Kaya A Fafatawar Cin Kofin Zakarun Nahiyar TuraiShi kuwa Mr. Vichai, wanda shi ne mamallakin kungiyar ta Leicester, hamshakin mai kudi ne mai shekaru 60 da haihuwa ya na da mata guda da yara hudu, ya mallaki kulob din ne a shekara ta 2010 akan kudi fan miliyan (£36).
A karkashinsa, kungiyar ta lashe gasar Firimiya lig na kasar Ingila a shekara ta 2016.
A wata sanarwa da ta fito daga Kungiyar Leicester City, ta nuna damuwarta kwarai da gaske, ta kuma kara da cewar tana tare da mamacin Mr Vichai da dukkannin wadanda hatsarin ya rutsa da su.
Your browser doesn’t support HTML5