Kocin Arsenal Mikel Arteta Ya Kamu Da Cutar Coronavirus

Mikel Arteta

A wasu rahotanni da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta fitar a jiya Alhamis, ta bada tabbacin cewar kocin Kungiyar Mikel Arteta, ya kamu da cutar Coronavirus.

A kan haka Kungiyar ta killace Arteta domin samun kulawa da lafiyar sa inda yake karban magani.

Kungiyar ta Arsenal ta bakin Daraktan ta Vinai Venkatesham ya ce Arsenal zata bada goyan baya da kulawa tun daga kan Kocin, 'yan wasa da kuma jagororin Kungiyar, don ganin dawowar su filin motsa jiki nan bada jimawaba, bisa shawarar masu kula da lafiya

Wannan cutar ta Coronavirus ta addabi kasashen duniya, musamman 'yan wasan kwallon kafa da suka hada da 'yan wasan Leicester City guda uku Daniele Rugani na Juventus.

Inda wasu wasanni aka dakatar da su saboda wannan Annobar ta Coronavirus, hukumar kula da kwallon kafa da shirya gasar firimiya ta kasar Ingila, tana tataunawa kan wannan batu domin duba yuwar daga wasu wasanni.

Tun kafin bayyanar cutar a jikin Mikel a ranar Alhamis, an daga wasan da Arsenal zata fafata da Manchester City saboda tsoron Coronavirus.