Kasashe 4 Suka Rage A Gasar Zakarun Nahiyar Afrika

A cigaba da fafatawa da akeyi cikin gasar cin kofin zakarun kasashen Afirka na shekara ta 2019 a can kasar Masar.

Yanzu haka kungiyoyin kwallon kafa na kasashe hudu sun kai ga samun nasarar zuwa wasan zagaye na gaba wato na daf da karshe (Semi final) a turance.

Kasashen sun hada da Senegal wanda ta cire Benin a wasan Quarter Final daci 1-0, sai kuma Najeriya da ta samu nasarar cire Afirka ta Kudu da kwallaye 2-1.

Sauran kasashen kuwa sun hada da Tunisiya wace ta yi waje da Madagascar da kwallaye 3-0, sai kuma Aljeriya da ta fitar da Ivory Coasts daci 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka tashi 1-1.

A jaddawalin wasan gaba da za'a buga Senegal zasu hadu da Tunisiya ranar Lahadi 14/7/2019, da misalin karfe biyar na yammaci agogon Najeriya.

Da misalin karfe 8 na yammacin ranar Lahadin kuwa Aljeriya ce zata barje gumi da Najeriya.