Kasar Korea Ta Kudu Zata Horas Da Masu Shirya Fina-finai a Najeriya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim

kasar Koriya ta kudu ta bada albashin da za a biya duk wandada zasu koyar da mutane harkar fim inda zata turo da wani fitattacen mai hada fina-finan ta zasu kuma dauki dawainiyar sa a nan gida Nijeriya.

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim, shugaban kamfanin Moving Image kuma wanda ya kirkiro shirin baje koli na farko wato Kano indigenous languages film marketers and festival wanda ake kira KILAF ne ya bayyana haka a yayin zantawa da wakiliyar DandalinVOA.

Idan masu sauraron mu na biye da mu kuma basu manta ba a kwanaki mun tattauna da jigon dangane da shirye shiryen baje kolin da za’a gudanar a watan Oktoban wannan shekara.

Abdulkarim Muhammad ya ce tuni aka aika da takardun goron gayyata ga duk wata kasa da take da ofishin jakadanci a Nijeriya kimanin kasashen 35 ake kuma sa ran kasashe 20 zasu amsa gayyatar.

Ya kara da cewa kuma tuni kasar Nijar ta amince tare da bada makadan kasarta domin su baje kolinsu a yayin taron baje kolin fina-finai na KILAF da za’a gudanar a watan Oktoban wannan shekara.

Abdulkarim Muhammad ya bayyana cewa suna fatan cewar zasu samu hadin gwiwa daga gwamnatin Nijeriya, wajen samun goyon baya ko hadin gwiwa domin tabbatar da yiwuwar hakan.

Daga cikin abubuwan da za’a amfana dai akwai sashe na gasar da za’a fitar da gwani cikin wadanda suke hada fina-finai kuma zasu lashe wasu makudan kudade, sannan ya ce za’a samu wadannan kudade ne ta inda suka aikawa wasu bankuna takardun shigowa wannan al’amari domin a dama da su.

Daga karshe ya kara da cewa duk wadanda zasu shigar da fina-fina su akwai wasu kudaden kalilan da za’a biya sannan baya ga haka akwai bitoci da za’a gudanar a wannan baje kolin da za’a shirya a Nijeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasar Korea Ta Kudu Zata Horas Da Masu Shirya Fina-finai a Najeriya