Jadawalin Yadda Wasan Zakarun Nahiyar Afrika Zai Kaya A Bana

A nahiyar kasashen Afrika bangaren wasan kwallon kafa a yau Jumma'a 12 ga watan Afirilu 2019, za'a fidda Jadawalin rukuni rukuni na gasar cin kofin kwallon kafa a Nahiyar kasashen na 2019 wanda zai gudana a kasar Masar.

Kasashe 32 da suka fito daga Afrika zasu kece raini a gasar bisa tsarin rukuni 8, za'a gudanar da wannan taronne a Giza Pyramids dake Cairo, da misalin karfe bakwai na yammaci agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da kasar Chadi.

Kasashe 14 da suka fito daga cikin mambobin 54 dake karkashin hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Afrika (CAF), wanda suka taba samun nasarar lashe kofin, suna cikin wanda zasu fafata a gasar da suka hada da mai masaukin baki Egypt, wace ta lashe sau bakwai sai Cameroon, Ghana, Nigeria, DR Congo, Cote d’Ivoire Algeria, Ethiopia, Sudan, South Africa, Tunisia, Morocco, Congo-Brazzaville da kasar Zambia.

Akwai kuma kasashe shida Mali, Burkina Faso, Uganda, Guinea, Libya da Senegal wanda suka taba kaiwa wasan karshe amman basu samu nasarar lashe wa ba suna cikin wanda za'a fafata dasu.

Bisa tsari an fidda tukunya tukunya har guda hudu wanda daga cikine za'a dauko kasashe domin sanya su cikin rukunin da suka fada.

A tukunya ta farko akwai Egypt, Cameroon, Senegal, Tunisia, Nigeria, Morocco.

Tukunya ta biyu kuwa DR Congo, Ghana, Mali, Cote d’Ivoire, Guinea, Algeria.

Sai tukunya ta uku wadda ta kunshi South Africa, Uganda, Benin Republic, Mauritania, Madagascar, Kenya.

Ta karshe itace tukunya ta hudu Zimbabwe, Namibia, Guinea Bissau, Angola, Tanzania, Burundi. Kuma wannan shine karo na 32 cikin gasar da akeyi na Nahiyar Afrika bisa tarihi.