A wannan zamani da muke ciki na wayewar kai, kamata yayi ace kowace mace ta samu ilimi don halin yau da kullun.
Ba wai zuwa makaranta don yin ilimin da za’ace mace ta samu aikinyi ba, mata kan iya amfani da iliminsu na kowane irin fanni a rayuwa don taimakama wasu mata dama al’uma baki daya.
A irin wannna kira na neman ilimi da wata Ungozoma gargajiya tayi Hajiya Attine, ta kasance tafara wannna aikin taimakama mata ne bayan wata ‘yar kwarya-kwaryar horaswa da suka samu daga gwamnatin jihar Kano shekarun baya.
Takan taimakama mata masu haihuwa wajen samun haihuwa me sauki, don wasu basu da halin zuwa asibiti ko dan wasu dalilai, don haka tana ganin idan har mata zasu kokarin ilmantar da kansu, wajen sanin yadda yakamata su taimaka ma ‘yan’uwansu mata to lallai wannan zaitai maka matuka wajen rage yawan mace mace da ake samu a wajen haihuwa, kuma za’a dinga samu yara masu lafiya bayan haihuwa.
Don haka samun wannna ilimin na Ungozoma na da matukar mahinmanci, wajen bama mai ciki shawarar abubuwan da suka kamata tayi yayin juna biyu, dama abubuwan da suka kamata taci don samun ingantaciyar lafiya da ita da abun da ke cikin.