Ga Yadda Hada-Hadar Zaratan Kwallon Duniya Ke Gudana

A cigaba da zawarcin zaratan 'yan wasan kwallon na duniya da kungiyoyi ke yi, don tun karar kakar wasanni na shekarar 2019/20, kungiyar Manchester United tana shiri don neman dan wasan Barcelona, Samuel Umtiti dan shekaru 25 da haihuwa.

Wasu rahotanni kuwa na nuna cewar akwai yiwuwar Manchester United za ta fasa sayar dan wasanta Romelua Lukaku, wanda kulob din Inter Milan take zawarcin sa a kan kudi fam miliyan £62.7.

Dan wasan Manchester City dan kasar Jamus, Leroy Sane, mai shekaru 23 a duniya yana daya daga cikin manyan 'yan wasan da kungiyar Bayern Munich take zawarci duk da cewa tana fuskantar kalubale wajen kammala cinikin dan wasan, hakan yana faruwa ne a daidai lokacin da Chelsea ta ki amince wa da tayin da Bayern Munich ta yi wa dan wasanta Callum Hudson-Odoi.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa na Celtic Neil Lennon ya shaida wa Arsenal cewa ta tanadi kudi mai yawa, idan tana son saye dan wasanta dan kasar Scotland, Kieran Tierney, mai shekara 22 a duniya.

Sai dai ita kuma Arsenal din a bangaren sayen 'yan wasan bana, ta ware fam miliyan £45, ne kacal wa kocinta domin ya sayo 'yan wasa wanda ake ganin zai yi wahala wa kungiyar ta saye 'yan wasa masu tsadda matukar bata sayar da na taba.

Har ila yau Arsenal din tana zawarcin dan wasan Monaco Keita Balde, mai shekara 24, da haihuwa bayan da Inter Milan ta fasa sayen dan kwallon na Senegal.