Dubun Mourinho Ta Cika A Kungiyar Manchester United

Tsohon kocin kungiyar Manchester United, Jose Mourinho.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dake kasar Ingila ta bada sanarwar sallamar kocinta Jose Morinho, bayan ya shafe shekaru biyu da rabi cikin kwantirakinsa na shekara uku da ya rattaba hanu.

Jose Morinho mai shekaru 55 da haihuwa dan kasar Putugal ya kama aiki a kungiyar a shekara 2016, inda ya maye gurbin Louis Van Gaal, ya samu nasarar lashe kofin kalu bale na Ingila da kuma Europe League, na Nahiyar Turai.

Kungiyar tace ta sallame shine saboda ba wani cigaba da yanzu takeyi musamman a wasan firimiya lig na bana, inda a ranar Lahadi Liverpool ta lallasa ta da ci 3-1 wanda hakan ya sanya ta a matsayi na 6 a teburin a wasan mako na 17 da maki 26, banbancin maki 19 tsakanisu da Liverpool wanda take saman tebur.

Kungiyar ta kashe kusan fam miliyan dari hudu wajan sayen 'yan wasan da suka kai 11, duk da haka hukumomi a kulob din sunce basa jin dadin yadda yake tafiyar da kungiyar, har ya kaima matasan 'yan wasa basa sha'awar zuwa kungiyar.

Kungiyar tace zata nada sabon kocin mai rukon kwarya kafin wasan da Manchester United za tayi da Cardiff City ranar 22 ga watan Disamba.