Billie Eilish Ta Lashe Kyaututtuka 5 A fagen Waka

Matashiya Billie Eilish

Fitacciyar mawakiya Billie Eilish ta samu lambobin yabo na "Grammys" guda biyar a jiya Lahadi, a dai-dai lokacin da duniyar kade-kade ke makokin mutuwar tsohon tauraron kwallon kwando Kobe Bryant, inda wasu suka dinga rubuta sakkonin ta'aziyya da tunawa da mamacin.

Matashiyar Eilish, mai shekaru 18 da haihuwa, ta samu manyan lambobin yabo guda huduciki har da wakokinta da su ka fi fice a shekarar, da kuma sabuwar mawakiya ta shekarar.

Da 'yan jarida su ka tambaye ta to "me zai ya biyo baya kuma? sai ta ce ban sani ba, abin da kawai ni ke tunani shine kasancewa ta a inda ni ke yanzu. Lizzo, daya daga cikin wadanda su ka goga da Eilish, wadda ta sami lambobin yabo guda 3, ta halarci bikin galar da aka yi a Staples Center dake birnin Los Angeles inda ta karrama marigayi Kobe Bryant da lambobin yabon da ta samu.