Ba Mamaki Mikel Arteta Ya Zama Sabon Kocin Arsenal

Tsohon Dan wasa Mikel Arteta

A yunkurinta na ganin ta yi sabon koci, Kungiyar lauyoyi ta Arsenal ta tuntubi
takwarorin ta na Manchester City akan Mikel Arteta, ya zama kocin kulob din a gaba, amma har yanzu dai babu wata yarjejeniya da aka cimma.

Wasu rahotanni na cewar Arteta, zai yi gaisuwar ban kwana ga ma'aikatan Manchester City, kasancewa ana hasashen za'a bayyana shi a hukumance a ranar Juma'a amatsayin mai horas da 'yan wasan Arsenal, inda zai maye gurbin Unai Emery da aka sallama a kwanakin baya.

Arteta dan asalin kasar Spain, yana da sauran ragowar kwantirakinsa a Manchester City, inda har yanzu take jiran Arsenal domin su tsaida yarjejiniyar kudi kafin ya tafi.

Arteta tsohon dan wasane a kungiyar Arsrnal, inda ya buga mata wasannin 150, tun daga shekarar 2011 har zuwa 2016.