Anya Victor Ba Zai Canza Sheka A Kakar Wasannin Bana Ba?

Tsohon dan wasan tsakiya na kasar Ghana Michael Essien, ya bada shawara ga tsohon dan wasan Super Eagles na Najeriya Victor Moses, da yayi amfani da damarsa a watan Janairu da zaran an bude hada hadar saye da sayarwar 'yan wasa na ganin ya canja sheka.

Zuwa wata kungiyar da ya kamata ya samun kansa, cikin wasanni masu zuwa a mai makon zama a kungiyar Chelsea wadda bata sanya shi a wasanni.

Dan wasan Victor Moses, ya buga wasa biyu ne kacal a wannan kakar wasan firimiya na bana cikin mako na 19, karkashin jagorancin kocinta Sarri.

Michael Essien wanda shima tsohon dan wasan Chelsea ne yace da zarar dan wasa baya samun kansa a masu buga wasanni, to dole zai sanya kansa a damuwa don haka ya kamata Moses ya canja sheka yadda za'ayi dashi kawai.

Ya kara da cewar duk wani dan wasa ya na son zuwa kungiyar Chelsea, amman abunda ke faruwa daga karshe mai horas da 'yan wasa ya kan zabi wanda ya keso ne domin su buga masa wasanni.

Dan wasan Moses ya samu damar buga wasanni a kungiyar ta Chelsea kar kashin Jagoranci tsohon kocinta Antonio Conte.

Ana alakanta Moses da komawa kungiyoyin kwallon kafa musamman wanda suke Ingila da suka hada da Crystal Palace, West Ham United, da kuma
Wolverhampton Wanderers.