Ana Zargin Wani Matashi da Kona Motar Hukumar Hizba a Kano

Motar Hibah

Ana zargin wani saurayi me suna Auwal Iliyasu wanda akema lakani da (This Man) da cewar ya kona motar hukumar Hizba a jihar Kano. Shi dai wannan matashin ya karyata wannan zargin wanda yake cewar, shi dai ya taka sahun barawo ne, ya bayyanar da cewar shi babu aikin da yake sha’awa a rayuwa sa kamar aikin Hizba, don haka bazai yi irin wannan katobarar ba.

Ta bakin na shi Auwal, yace akwai wasu matasa da kanyi shaye-shaye a bayan gidansu wanda ya nuna musu da cewar yakamata su dena, wanda har ta kai sunyi uwaka-ubaka da wannan matasan. Don haka yanaganin kamar wadannan matasan ne sukayi wannan aikin, ya yi nuni dacewar an tursasamasa da ya aminta dacewar shiyayi wannan lafin wanda yasa yace yayi amma a zahirin gaskiya bai aikta wannan laifin ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Kona Motar Hizba a Kano - 1.55"