Kocin kungiyar Arsenal Wenger ya ce mumunan kuskurene amfani da na'urar Mataimakin alkalin wasa ta (VAR) a gasar Firimiya lig mai zuwa inda kungiyoyin kwallon Kafa na Ingila suka amince da amfani da na'urar saboda rekice-rikicen da na’urar ke tare dashi.
Wenger ya goyi bayan ayi amfani da na'uran ne bayan an tashi daga wasan da kungiyarsa ta Arsenal ta sha kashi a hannun Newcastle 2-1 a wasan mako na 34 a Firimiya lig.
Wenger, ya bayyana cewar da anyi amfani da na'urar da zani zakulo wata bugun daga kai sai mai tsaron gida da ya kamata a basu yayin da danwasan Pierre-Emerick Aubameyang, ya buga wata kwallon da ta taba hannun dan wasan baya na Newcastle.
Wenger ya ce yana goyan bayan ayi amfani da VAR a kakar wasan shekara mai zuwa.
⚽⚽ Kungiyar Monaco, ta ce zata sake bada dama wajan sabunta kwantirakin dan wasan tsakiyarta Thomas Lemar 22 a wannan shekarar wanda kungiyoyin Arsenal da Liverpool suke zawarcin
Newcastle ta ce ta shirya tsaf domin sayen mai tsaron raga Sparta Braga mai suna Martin Dubravka a matsayin dindindin a kulob din maimakon zaman aro da yake yi a kungiyar.
Aston Villa da Celtic sun jera sahu guda wajan zawarcin dan wasan baya daga kungiyar, Yeovil Town's dan kasar Wales mai suna Tom James.
Kocin Crystal palace, Roy Hodgson ya nuna nadama akan rashin iya rinjayar Wilfried, Zaha ya buga wasa a kasar Ingila a maimakon Ivory Coast.