Akwai Bukatar Inganta Filayen Wasannin Cikin Gida

Filin Wasan Jihar Bauchi

Anyi kira ga Gawmnatin jihar Bauchi da ta taimaka don ganin an kammala gyara Filin wasa na tunawa da Sir Abubakar Tafawa Balewa.

Filin wasanni na Abubakar Tafawa Balewa (Stadium) dake jihar Bauchi a tarayyar Najeriya, yana tsaye cak daga gyare gyaren da aka fara shekarun baya.

Kan hakane Al'umman jihar Bauchi musamman magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist suke kira ga sabuwar Gwamnan jihar karkashin shugabancin Sanata Bala Muhammad, da ya taimaka ya cigaba da gyaran filin, domin Kungiyar tasu ta dawo buga wasanninta a gida, kasan tuwar nan ne babban filin ta da take gadara dashi.

Kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist dai ta shafe kakar wasanni biyu tana buga wasaninta a wasu jihohi, inda a 2017/18 tayi wasa a Jihar Filato, sai kuma 2018/19, ta buga a jihar Gombe, sakamakon rashin kammala gyaran da yaki ci yaki cinyewa.

Masu sha'awar kwallon kafa da magoya bayan kulob din na ganin cewar wadannan dalilan na daga cikin abubuwan da kan ke maida kungiyar baya.

Don haka akwai bukatar gwamnati ta duba wannan aikin da ganin an cigaba da gyara wannan filin wasan, kamar yadda sauran kungiyoyi na wasu jihohi ke da damar yin wasannin su a cikin jiha ba tare da sun fita jihohi makota ba.