Babban jami’in ‘yan sanda mai kula shalkwatar rundunar ‘yan sanda ta yankin zone ii dake jihar Legas Abdulmajid Ali, ya bukaci a mayar da tuhumar da ake wa wani mutu da ake zargi da sa wa Karen sa suna “Buhari” , shugaban ya bukaci a mayar da shari’ar ofishin sa ba tare da bata lokaci.
Kamar yadda mujallar Dailypost ta wallafa, mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya ce kawo yanzu ya kira wata ganawa da mutanen da abin shafa domin ganin yadda za’a kashe takaddamar dake tsakanin jama’ar da abin ya shafa.
An kama mutumin mai suna Joe Chinake kuma yana kulle a ofishin jami’an ‘yan sandan a Sango Otta dake jihar Ogun har na tsawon kwanaki uku bayan makwafcinsa ya kai kararsa da sawa Karen sa suna Buhari.
Koda shike Mr Chinakwe ya yi ikirarin cewa ya sanyawa Karen suna Buhari ne domin yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke burge shi.
Makwabcin nasa wanda jami’an ‘yan sanda suka bayyana mai suna Halilu Ummar ya fito daga jihar Sokoto ya bayyanawa jami’an cewa Mr Chinakwe ya sa wa Karen suna buhari ne domin neman ya ci masa zarafi a sakamakon sunan mahaifin sa Buhari.
Oyeyemi ya bayyana cewa ba lallai a tura lamarin kotu a yau litini ba tunda IG ya nuna ra’ayin sasanci a tsakanin mutanen biyu.