Kamar yadda muka saba a kowane karshen mako, shirin samartaka na dandalin voa na kebe lokaci domin zantawa da samari da 'yan mata domin jin ra'ayoyi mabambanta musamman a halayen zamantakewa, soyayya da kuma bada shawarwari daga bakin iyaye da kwararru domin samun daidaito da bin hanyar data dace.
A wannan karon mun nemi jin tabakin samarinne akan wata sabuwar dabi'a ta share tsawon dare ana chattin ko waya da juna harma a wasu lokuta sukan aikawa da juna hotuna da video kuma duk da sunan soyayya.
Kodashike masu iya magana sunce abincin wani gubar wani, wannan magana haka take domin kuwa kashi tamanin cikin dari na samarin da muka zanta dasu sun nuna cewa a ganinsu ba wani abin damuwa bane ka raba dare kana zance domin a cewar su tafiya da zamani itace hanyar da ta dace.
Sai dai kuma 'yan matan sun nuna cewar a nasu ra'ayin sun gwammace su hadu ido da ido a koda yaushe domin hakan ya fi kara dankon soyayya, domin a cewar su waya cikin dare babu abin da take haifarwa banda rashin kunya.
Daya daga cikin wadannan 'yan mata ta bayyana cewa bata taba sanin cewa samari basa da kunya ba sai da tafara wayar dare ko free call sa'annan abin ya bata mamaki domin wasu maganganun da suke fitowa daga bakin saurayin ko kare bazai ciba.
A cigaba da kasancewa tare da mu domin jin yadda hirar ta kasance, kuma za'a iya sauraren hirar kai tsaye a shafinnu na www.dandalinvoa.com a dai dai kan kowace sa'a. idan aka bude shafin za'a ga inda aka rubuta LIVE:Dandalinvoa, a latsa wurin domin sauraren shirin.