Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharudda Don Cin Jarabawar Ganawar Daukan Aiki “Interview”!


Hannu Da Hannu
Hannu Da Hannu

Akwai abubuwa muhimai da yakamata mutane su bama hankalin su da kulawa ta musamman, da dama mutane basa lura da yadda suke gaisawa da mutane wajen bada hannu. Da yawa rashin iya gaisawa da mutane kan sa mutun yarasa aikin shi, ko kuma ya saka mutun cikin wani hali.

Masana hallayan dan’adam sun bayyanar da wani rahoto da ya jaddada muhimancin mutane su dinga lura da yadda suke gaisawa da mutane, domin kowane irin mutun da irin yadda ake gaida shi, yadda mutun zai gaisa da abokin shi ya banbanta da yadda zai gaisa da mutanen a lokacin da aka gayyace shi ganawar daukan aiki “Interview” haka da yadda mutun zai gaida shugaban shi a wajen aiki.

Da yawa mutane kan mika hannu batare da nuna wani alama na girmamawa ba, ko kuma mutun ya gaisa da mutun yana murda hannun mutun da dai wasu abubuwa da basu kamata mutun yayi ba, wanda hakan yana iya bayyana ma mutane wasu abubuwa dangane da kai. Don haka yake da muhimanci idan mutun zai gaisa da mutane yasan suwa yake gaisawa da su don gujema abun magana.

Haka kada mutun ya gaisa da mutane ya rike musu hannu da ya wuce na tsawon dakika biyu zuwa uku, akwai bukatar mutun ya rike hannun mutane da muhimanci da karfi batare da matse hannun ba, hakan yana nuna ma mutun cewar wannan mutumin yana da kuzari da azama koda an dauke shi aiki zai iya gabatar da aikin shi batare da ragwanci ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG