Hukumar "NASA" Ta Duniya Na Yunkurin Zuwa Duniyar Jupiter!

Duniyar Jupiter.

Hukumar binciken halitun sararrin samaniya ta duniya “NASA” na gudanara da wani bincike da su kayima lakani da “JUNO” wannan binciken an kaddamar da shi ne 5, ga watan Ogustan shekarar 2011, da burin kamala shi a ranar 4 ga watan Yuli 2016.

Babban burin su shine, su kai ga duniyar “Jupiter” wanda a tarihin duniya babu wani mahaluki, ko wani kirkirar na dan'adam da ya taba kaiwa koda kusa da ita. Domin zuwa kusa da duniyar, wani abune mai matukar wahala. Tana da nisan kimanin murabba’I milliyan ashirin daga sauran duniyoyi.

Kusantar ta ma na dauke da wasu haddura, don wani irin zafi da burbushin wuta da take fesowa, hakan yasa zuwa wannan duniyar yake da matukar hadari ga rayuwar dan’adam. Amma sun ci alwashin kafa tarihi.