Wannan wani abun dubawa ne da idon basira. Hukumar kula da yara ta majalisar dinkin duniya wato “UNICEF” ta fitar da wani rahoto mai ban tsoro, wanda ta bayyanar da cewar kimanin yara sama da milliyan hamsin 50M, ne a kasar Najeriya, basu samun damar amfani da Ban-daki wato “Bayi” don biyan bukatun su.
Hukumar ta kara da cewar kasar Najeriya itace kasa ta biyar a jerin kasashe a duniya da suke fama da wannan matsalar. An bayyanar da hakan ne a wata kasida da mataimakiyar hukumar ta kasa, data bayyanar Ms. Ijeoma Onuoha, a lokacin da ake bukin zagayowar ranar bayi, tsaftar muhalli da ruwan sha na duniya.
An bayyanar da wannan a matsayin babar matsala da take haifar da mafi akasarin cuttutuka, da ake fama da su a kasar. Domin kuwa mutane da dama su kanyi amfani wasu kango, wajen biyan bukatun su, batare da damuwa da irin hali da mutane zasu shiga ba a sanadiyyar bata yanayin iskar da mutane ke shaka.
Don haka ana kara kira da babbar murya, mutane su kokarta su dena amdani da kango, hanyoyi, da sauran guraren da mutane suke mu’amalar yau da kullun, don biyan bukatun su, domin hakan shike haifar da mafi akasarin cuttutuka dake addabar jama’a a kasar.