Ma'aikacin Kashe Gobara Ya Samu Canjin Fuska Na Farko A Duniya

Canjin Fuska Patrick

A karon farko a duniya anyi ma Mr. Patrick Hardison, canjin fuska, wannan shine aiki na farko da aka tabayi, da aka cire fatar fuskar wani aka maida ma wani mai rai. Mr. Patrick, tsohon ma’aikacin kwana-kwana ne, wato masu kashe gobara, a jihar Mississippi, ta nan kasar Amurka.

A shekarar 2001 ne suka tafi wani gida da ya kama da wuta don kashe gobara, sai mai gidan yace matar shi tana ciki, a dai-dai lokacin da Patrick, ya shiga don ceto ran matar, sai katako daga sama ya fado mishi, hakan yasa fuskar shi ta kone. Tun bayan haka anyi mishi aiki a fuskar shi sau da yawa amma ba’a taba samun nasara ba.

Wani fitattaccen likitan fata yayi alkawalin idan aka samu fuska da tayi dai-dai da ta Patrick, to shi zai iya saka mishi fuskar. Ana cikin haka sai ga wani matshi Hardison mai shekaru 26, dan tseren keke ya fadi ta kai ya mutu, iyayen shi suka bada fuskar shi. Akalla shirye-shiryen yin wannan aiki, na cire fuskar matashin don maida ta ga Partick, ya dauki likitocin shekara daya. Wanda suka shiga dakin aikin suka kwashe awowi 26, da ma’aikata 150.

Wannan aikin da akayi na canza fuskar wani zuwa gawani shine na farko, da aka taba yi a duniya kuma akayi nasara. Mr. Patrick, dai yana cigaba da samun sauki a sibiti, kuma yayi magana da manema labarai, inda ya bayyana musu cewar baitaba tsanmanin zai samu lafiya kamar yadda yake yanzu ba. Kuma yana kara gode ma likitocin da sauran al’uma da wannan nasarar.