Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zai Yi Gogaiya Da Studio Daban Daban A Harkar Fina Finai


Abubakar Adamu Abdullahi Darakta
Abubakar Adamu Abdullahi Darakta

A shirin mu na nishadi a yau Abubakar Adamu Abdullahi ya sake dawowa bayan tattaunawar da Dandalin Voa yayi da shi shekarun da suka gabata.

Abubakar G-boy ya ce kawo yanzu ya bude studio na sa na kashin kansa inda ya ke aikin daukar hoto tare da ba da umarni a lokacin da ake nadar fina finai.

A cewarsa yana sa ransa zuwa wata sabuwar shekara idan yana raye yana da burin bunkasa sana'ar ta sa, inda ya ke fatan ya zama international studio da zai yi gogaiya da studio daban daban daya jibanci harkar fina finai.

A fannin tsegumi kuwa Yakubu Muhammad na Lagos faggen daukar fim din turanci na Nollywood mai suna Hotel April , shi kuwa Aminu Saira ya shirya tsaf domin fara aikin daukar fim din Labarin Gobe.

XS
SM
MD
LG