Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Young Star Luda Bauchi Ta Lashe Kofin Hon Bala Mato Zungur


Young Star Luda Bauchi

Kungiyar kwallon kafa ta Young Star Luda, dake karamar hukumar Bauchi jihar Bauchi, a tarayyar Najeriya, ta samu nasarar lashe kofin kwallon kafa na Hon Bala Mato Zungur Cup 2018, wanda aka sa a garin Luda dake Liman Katagum.

Kungiyar ta Young Star Luda ta samu nasarar doke takwararta Juwara Young Planners Fc da ci 1-0 a wasan karshe da aka buga ranar laraba 5/9/2018 a garin Luda.

An bada manyan kyautuktuka bayan an tashi daga wasan, kungiyar da ta samu nasara Young Star Luda, ta sami Kyautar Rigunan ‘yan wasa (Jeysey) da kuma Kwallo (Ball) sai wadda ta zo na biyu Juwara Fc, ta ma aka bata Kyautar Rigunan (Jeysey).

Wacce tazo matsayi na uku Young Tiger Luda Fc, kuma ta samu Kyautar kwallayen bugawa (Balls) bayan da ta lallasa takwararta Gamawa United daci 3-1.

Bayan kammala wasan wakilin Dandalinvoa a Bauchi da ya halarci taron ya kuma zanta da wasu a wajan wanda suka hada da Kocin kungiyar kwallon kafa ta Young Star Luda wacce ta samu nasara mai suna Isma'il AC, da kuma Kaftin na kungiyar Juwara Fc, wacce ta zo ta biyu, Ayuba Mata,tare da shugaban kwamitin da ya shirya wannan gasa Usman Dunga Luda, inda dukkansu sukayi gode game da kammala wasan lafiya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG