Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samuel Eto'o Ya Taka Rawar Gani


Samuel Eto'o

Samuel Eto'o ya kawo wa Norbert Owona dauki inda yayi mishi alkawarin sabon gida, saboda irin rawar da ya taka a baya.

Tsohon jagaran yan wasan kallon kafar kungiyar Kasar Kamaru Norbert Owona, wanda ya kwashe shekaru biyu bashi da gidan zama, ya samu kyautar gida daga Samuel Eto'o tauraron kallon kafa dan kasar Kamaru.

kasancewar ba kasashen Afirka kawai, bane suke fuskantar irin wannan barazanar.Inda a turai ma ka iya ganin mutane suna kwana akan tituna domin rashin wajen zama.

Samuel Eto'o ya kawo wa Norbert Owona dauki inda yayi mishi alkawarin sabon gida, saboda irin rawar da ya taka a baya. Owana ya mika godiyar shi ga Eto'o a lokacin da yayi mashi albishir da wannan kyautar bayan ya ziyarce shi a asibiti inda yake kwance yanzu haka yana jiran ayi mashi aiki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG