Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Fafatawa A Gasar Kwallon Kafa Ta Mata Karo Na Takwas


Kwallon Kafa Na Mata

A cigaba da fafatawa da akeyi cikin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, ajin Mata na shekara ta 2019 karo na 8 (Eighth Edition) a can kasar Faransa.

A yau Jumma'a 14 ga watan Yuni 2019 kasashe shida daga bangaren rukuni daban zasu kece raini a matakin wasan rukuni zagaye na uku.

Kasar Japan zasu kece raini da Scotland, sai kuma Jamaica da Itali, da misalin karfe biyar na yammaci

Wasan da za'a fafata da misalin karfe takwas na yammaci agogon Najeriya, tsakanin 'yan matan kasar Ingila da Ajantina shine zai dau hankalin 'yan kallo, ganin cewar a shekarar 2007 cikin gasar ta cin kofin Mata wacce kasar Sin ta dauki nauyi, Ingila ta lallasa Ajantina da kwallaye 6 da1 wasan rukuni.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG