Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanzu Haka Kusan Kashi Tasa’in Na Garin a Kone Yake


Gwamns Kashim Shettima
Gwamns Kashim Shettima

Gwamna jihar Borno Kashim Shattima, ya yabawa rundunar Sojojin Najeriya, saboda kokarin da suka yi na sake kwato wasu garuruwa dake hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.

Gwamnan yayi wannan yabon ne a lokacin da ya ziraci garin Bama, daya daga cikin garuruwan da ‘yan kungiyar Boko Haram, suka yi kaka gida a ciki kusan kimanin watani Takwas da suka gabata.

Gwamnan yace akwai bukatar taimakon gaggawa a irin wadannan garuruwa da aka lalata masammam garin Bama, da yanzu haka kusan kashi tasa’in cikin dari n garin a kone yake.

Garin Bama dai na cikin manyan garuruwan dake jihar Borno, da ‘yan Boko Haram suka kona, shi kansa Shehun Bama Alhaji Kyari Ibn El-Kenemi, ya ronki Gwamnati jihar da ta kawowa garin dauki.

XS
SM
MD
LG