Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudu Ba’a Tsira Ba

LAPD surround a house where a man armed with a rifle barricaded himself, in Los Angeles, California June 9, 2014. The man, who led police on a chase from East Los Angeles to North Hollywood, was wanted for making threats and has been taken into custody af

Matashi ‘dan shekaru goma sha takwas da haihuwa ya tsere wa ‘yan sanda a Arewa maso gashin jihar Ohio, amma ya kawo kansa gurun ‘yan sandan lokacin daya dawo neman hularsa da ya yarda a wajen da ya aikata laifin.

Wata kungiyar yada labarai ta Arewa maso Yammacin jihar Ohio ce ta fitar da wannan labari, inda tace ‘yan sandan sunyi kokarin tsayar da matashin mai suna Montgomery alokacin da yaki bin umarnin fitila mai baiwa motoci hannu akan tituna ranar talatar data wuce, ya kuma kara wuta a motar sa Allah ya bashi dama har ya tsere wa jami’an ‘yan sandan da suka biyo shi, daga baya ya shiga wani lungu inda ya bar motar da yake tukawa ya taka a kafa.

‘yan sanda sunce sun dakatar da shi alokacin da yake tafiya a kafa, ya kuma gayawa jami’an cewa yana kan hanyar sa ne domin ziyartar abokin sa amma basu kama shi ba.

Daga baya ne Montgomery ya dawo gurin da ya aikata laifin domin neman hular sa daya yarda, inda ya baiwa ‘yan sandan fasalin hular da yake nema daga jin haka suka kame shi domin sun ga lokacin da hular ta fadi alokacin da matashin ya aikata laifin.

XS
SM
MD
LG