Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Ta Kaya A Wasannin Premier League


Masu rike da kofin zakarun turai wato champions league Bacerlona sun yi waje road a gasar ta bana sakamakon kashin da Atletico Madrid ta bata da ci biyu da nema a jiya laraba a wasan su na farko a matakin kwata final a makon jiya.

Bacerlona ce ta doke Atletico da ci 2 - 1 wanda ya bada jimlar sakamakon ya zuwa ci uku da biyu da Atletico din ta yi galaba, wannan dai tarihi ne ya mai maita kansa domin kuwa a shekara ta 2014 ma Atletico din ce ta fitar da Barcelona a matakin kusa da na karshe inda ta doke ta da ci 2 - 1.

A bangare daya kuma Beyern Munich ce ta doke Benfica bayan da wasan su ya karkare a kunnen doki da ci 2 - 2, wato kenan ci 3 - 2 inda Munich din ta yi galaba. Manchester city ma ta sami tsallakewa zuwa wasan kusa da na karshen bayan da ta doke PSG ci daya da nema bayan da wasan su na farko ya karkare da kunnen doki da ci 2 - 2.

Kungiya ta hudu kuma da ta sami tsallakewa ita ce Real Madrid wacce ta doke Weburg da ci uku da nema, bayan da ta sha kashi a wasan su na farko da ci biyu da nema.

Hukumar bada tallafai ta duniya na binciken zarge zargen almundahana a wani asusun bada tallafi da shahararren dan wasan nan na Ivory cost Drogba ya kafa, wata jarida mai suna Daily Mail ce tayi zargin cewa daga cikin tsabar kudi fan miliyan daya da dubu dari bakwai da asusun na Drogba ya sami tarawa domin bada taimako ga mabukata, fan dubu 14 da dari hudu ne kadai aka rarraba a matsayin tallafi a Afirka.

Sai dai dan wasan mai shekaru 38 yayi barazanar gurfanar da jaridar a gaban kotu bisa zargin bata masa suna, a wata sanarwa da ya fitar ya musanta almundahana ko sama da fadi da ayyukan cin hanci da rashawa a wannan asusun nashi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG