Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hannun Daya Baya Daukar Jinka Messi


Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, ta lallasa kungiyar wasan kwallon kafa ta Barcelona, da ci biyu da nema a wasan kwata fainal a gasar zakaru wanda aka buga a Madrid.

Hannun daya baya daukar jinka ya nuna inda dan Kasar Argentina, kuma dan wasan gaba na Bercelona Lionel Messi, ya kasa yin nasarar yin abinda ya saba domin a wannan karon Madrid, ta dage.

A karawarsu a zagayen farko Bercelona, ta doke Madrid da ci biyu da daya .

Ita kuwa Bayern Munich, ta kasar Jamus, ta sami kaiwa ga wasan kusa dana karshe ne bayan da tayi waje rod da Benfica ta Lisbon, da jimilar kwallaye uku da biyu a gasar ta zakaru.

Atletico Madrid, ta takawa Bercelona mai rike da gambin birki inda ta hanata kaiwa ga wasan kusa dana karshe duka da irin taka ledar da Bercelona , tayi sha kashi.

XS
SM
MD
LG