Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Abokantaka Take Tsakanin Matasa A Wannan Zamani


An Fafata Wasan Sada Zumunci Tsakanin Kungiyar Matasa Ta PDP Social Media Da APC Social Media Jihar Gombe
An Fafata Wasan Sada Zumunci Tsakanin Kungiyar Matasa Ta PDP Social Media Da APC Social Media Jihar Gombe

Abokanta ko aminantaka tsakanin matasa wani abu ne mai muhimmancin gaske wanda wasu lokuta mutane kan ‘dauke ta a matsayin ‘yan uwanci.

Ahmad Abubakar Dakta na jami’ar Bayero dake Kano, ya kara haske kan yadda abokanta take tsakanin matasa a wannan zamani da kuma zamanin baya. Inda yace akwai banbanci tsakanin abokantaka ta zamanin baya da kuma abokantaka irin ta wannan zamanin.

Amintaka dai na kulluwa ne tsakannin mutane biyu da tunaninsu yazo iri daya, kuma zasu iya zama tattauna kan wani batu da kowa ya amince, abokanta kuwa itace idan ra’ayin mutane biyu yazo ‘daya ake zama ana fahimtar juna.

A wannan zamanin akan sami mutane suna abotaka domin morar wani abin duniya, wasu lokuta kuma da zarar bukatar mutum ta biya ya sami abin da yake nema to shikenan abokanta zata fara dusashewa, sabanin yadda ake a zamanin baya wadda take aminci ne wanda baya yankewa wanda ya hada da iyali baki daya.

Saurari cikakkiyar hirar Usman Kabara da Ahmad Abubakar Dakta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:58 0:00

XS
SM
MD
LG