Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalibai Su Hada Karatu Da Sana’a Shine Mafita A Wannan Zamanin


Kofar Jami'ar Bayero
Kofar Jami'ar Bayero

Kasancewar tsadar Jami’o’i a wannan zamani matasa da yawa ke kukan cewa basa iya biyan kudin makaranta, kuma basu da lokacin da zasu iya yin sana’a. A cewar Farfesa Ibrahim Malumfashi, na Jami’ar jihar Kaduna a Najeriya, wannan wata matsala ce da ta dade Arewacin Najeriya, kuma yanayin zamantakewar Hausawa da Fulani shine musabbabinta.

Ya ci gaba da cewa idan aka duba yadda bahaushe ya sabayi shine ya samarwa da ‘ya ‘yansa makwamci da abinci da ilimi da kuma sauran abubuwan rayuwa, yawanci ba a mayar da hankali wajen daura yara bisa ga sana’a, sai dai a tabbatar sunyi karatu sun kammala har sun sami aikin gwamnati.

Kasancewar zamani na zuwa da canje canje, yanzu haka zamani ya canza wannan tsari da ake aiki da shi baya aiki, domin idan har mutum ya kammala karatun wasu lokuta samun aiki kan yi wahala.

A cewar wani mai tsokaci akan al’amura Ahmad Abubakar Dakta, kuma ‘dalibi a jami’ar Bayero ta jihar Kano. Yace ‘dalibai Hausawa basa amfani da damarsu wajen hada sana’a da karatu sabanin sauran ‘dalibai musamman na Kudancin Najeriya.

Saurari cikakkiyar hirar Usman da Maryam da kuma bakinsu, Farfesa Ibrahim Malumfashi da Ahmad Abubakar Dakta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00

XS
SM
MD
LG