Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsunto Wani Mutun Da Ya Kwashe Shekaru 40 A Dokar Daji!


Mutun Ma'abuci Namun Daji
Mutun Ma'abuci Namun Daji

A karni na ashirin da daya 21, da muke cikin, Idan aka bama wasu labarin wani abu za suyi mamaki. Ga ma’abota kallon fina-finai, a ‘yan shekarun baya, anyi wani fim mai suna “Tarzan” wanda ya bayyanar da rayuwar wani mutun a cikin daji, wanda dabi'un shi na dabbobi daji ne.

A yankin wani tsuburi na “Quang Ngai” a kasar Vietnam, wani mutumi yayi gudun tsira cikin kungurmin daji, tun a lokacin yakin basasa na Vietnam, a shekarar 1972. Bai sake dawowa cikin jama’a ba, ya kwashe tsawon rayuwar shi cikin daji da rayuwa irin ta namun daji.

Wasu jerin manazarta da suka shiga cikin dajin, da babu mahaluki da ya taba shiga ya fito, sai gashi sun tsinci wannan mutumin, sunyi kokarin yin magana da shi, bai san abun da suke cewa ba. Bayan gudanar da bincike sun iya gano cewar, ya kwashe tsawon sama da shekaru arba’in zuwa arba’in da hudu, a cikin dokar daji shi kadai.

Allah ya bashi basira, wanda ya gina gidan kara, kuma yana cin abinci daga farauta da ya keyi na namun daji. Wata baiwa da yake da wanda yake iya kama tsuntsu, ko bera da sauri fiye da yadda mutun zai dannan a yanar gizo don binciken wani abu.

Baki daya rayuwar shi a cikin dajin yayi ta, wanda bai san mutane ba, bai iya rayuwa ta mutane ba, yana amfani da ganyen itace don suturta jikin shi. Bai iya magana ba, sai dai kukan tsuntaye, da na sauran namun daji. Yanzu haka dai yana hannun hukumomi, inda ake kokarin duba lafiyar shi da bashi duk taimako da yake bukata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG