Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Zai Ratsa Tsakiyar Duniya


Masana kimiyya sun bayyana wani hasashe nasu dake nuni da cewar a ranar Juma’a mai zuwa Wata zai yi zazzabi wanda zai yi jajawur, mai zafi da ba’a samu irin sa ba a wannan karnin.

Hukumar binciken sararin sama ta Amurka, NASA ta tabbatar da cewar wata a ranar zaiyi ja har na tsawon awa 1 da mintoci 43, mutane a yankin gabashin Afrika, da kasashen tsakiyar Asiya, zasu ga wannan kusan fiye da sauran mutane a fadin duniya, sauran mutane kuwa a fadin duniya zasu ga kadan daga ciki na wata a wannan ranar.

Masanan sun tabbatar da cewar a kasar Amurka za’a fara ganin canjin da watan zai yi daga misalin karfe 4:21 na yamma, amma mutane da dama ba zasu samu damar kallon jan watan ba saboda hasken rana.

A lokacin da ake samun abkuwar wannan yanayin wanda Wata ke dai-daituwa da Rana, sai hasken Rana ya rufe na wata, don haka wata yana rasa adadin hasken da zai bukata, a sanadiyar rana bata da karfi.

Hakan yasa wata zaiyi ja don haka masana suka kira wannan yanayin wata mai na’uin jini. Masanan sun bayyana aukuwar hakan a ranar Juma’a a sanadiyar Wata na ratsa tsakiyar duniya, wanda hakan zai samar da inuwar duniya.

Wannan zai zama yanayi mafi tsawo fiye da yadda aka saba gani wanda wata keyin ja na kimanin minti 4, wannan zai dau lokaci mai tsawo.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG