Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Matashi Ya Tsallake Rijiya Da Baya


Wani magidanci mai suna Austin Segun ya gamu da fushin jama’ar, al’umar Eruemukohwarien, dake karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta, inda suka nakada mashi duka bisa fusatar da suka yi domin asabtar da dansa mai shekaru goma sha uku (13), inda ya kona shi da dutsan guga.

Shi dai yaron mai suna Tobi mahaifin nasa ya daure shine har na tsawon kwanaki uku domin zargin cewa yaron nada maita, ‘yan sintirin al’umar Eruemukohwarien, ne suka ceto yaron.
Matar mahaifin yaron ta shedawa jaridar Vanguard cewa a Coci ne aka sheda masu cewa yaron nada maita, a cewarta wai yaron da bakinsa ya amsa.

Daga bisa ‘yan Sanda ne suka ceci Austin Segun, mahaifin yaron daga hannun jama’ar da suka yima shi dukan kawo wuka daga bisani an bukaci Austin Segun, da ya bar garin.

Shi kuwa Tobi cewa yayi yana gudu daga gida saboda mahaifiyarsa ta rasu baya kuma jindadin zama a gida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG