Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Bom ya Sake Tashi a Kasuwar Potiskum


Tashin Boma-Bomai
Tashin Boma-Bomai

Wani bom ya tashi a kasuwar sayarda wayar salula a garin Potiskum, inda wata 'yar kunar baki wake 'yar kimani shekaru goma sha hudu ta tada bom din a lokacin da jami'an tsaron kasuwar suka hana ta shiga kasuwar.

Mutane shida ne suka rasa rayukansu a sandiyar tashin wannan bom din wanda ya hada da ita kanta 'yar kunar bakin waken, inda wasu kuma suka ji raunuka.

Kawo yanzu dai babu wani bayani daga jami'an Gwamnatin jihar Yobe, duk da tashin bom din harkokin kasuwanci sun cigaba a garin na Potiskum.

​##caption:Tashin Boma-Bomai. (File Photo)##

XS
SM
MD
LG