Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakoki Na Sun Raja'a Ne Wajan Hada Kan 'Yan Arewa - Inji Ahmad Rufa'i AKA-(Deezeel)


Hanya daya tilo da za a inganta harkar waka a arewacin Najeriya, ita ce ta hadin kan mawaka tare da tafiyar da waka kan matakin da ya dace tana kaiwa a yanzu, inji mawaki Ibrahim Ahmad Rufa’i wanda aka fi sani da Deezeel.

Deezeel, ya ce wakokinsa na waiwayar hanyar da za a inganta hadin kai domin a cewarsa, a yanzu kan ‘yan arewa a rarrabe yake haka kuma mawakan na da matsala musamman ta hanyar rashin tallata wakokinsu a arewa maimakon tallata na turawa kamar yadda ake yi a yanzu.

Daga karshe ya ce yana isar da sakonin nishadantarwa tare da ilmantar da al’umma, game da basu irin abinda suke so amma ta hanyar da ta dace.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:25 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG