Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsegumin Wannan Makon Na Kannywood


Jarumin Fina-Finan Hausa, Ali Nuhu
Jarumin Fina-Finan Hausa, Ali Nuhu

Tawagar babban Darakta Garba Kabara ta dawo gida Kano bayan kwashe kwanaki suna aikin wani shiri a gidan Talabijin na Gamji dake garin Gusau a jihar Zamfara.

A daya bangaren kuma jarumi Ali Nuhu ya cika sharuddan dake cikin kwantiragin da ya rattaba wa hannu na kamfanin SRK na aikin fim din Turai, jarumin dai zai yi aiki da jarumai kamar su Nabaraska, Hassan da Husaini, da Musa da Aisha ‘Dan Kano da Ibrahim Sharukan da dai sauransu.

Ranar Juma’a ne jarumi Sadiq S. Sadiq da Zainab Indomie suka sauka a Accra ta kasar Ghana, bisa gayyatar da aka yi musu kuma jaruman zasu kwashe kwanaki biyar a can babban birnin na Ghana suna cashewar sallah tare da Hausawan kasar.

Shima kuma jarumi Ali Nuhu da Jamila Nagudu na can birnin Yamai a jamhuriyar Nijar bisa gayyata, don taya masoya murnar kewayowar bukin karamar sallah, jaruman zasu kwashe kwanaki suna wasanni a wurare dabam dabam kafin su fara shirin dawo wa gida Najeriya.

XS
SM
MD
LG