Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta'aziyyar Jaruma A'isha Dan Kano


Ta'aziyyar Jaruma A'isha Dan Kano
Ta'aziyyar Jaruma A'isha Dan Kano

A jiya talata ne Allah Yayi wa sananniyar jarumar nan ta Kannywood Hajiya A'isha Dan Kano rasuwa bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya kimanin makwanni biyu, kuma an yi jana'izar ta a unguwar Gwammaja jahar Kano kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Ta dalilin haka ne Dandalin VOA ya ziyarci gidan mamaciyar, domin zantawa da 'yan uwa da abokan arziki domin jin yadda suka ji dangane da wannan babban rashi.

Jarumai da dama maza da mata sun halarta kuma sun bayyana irin rawar da jarumar ta taka a fagen wassannin Hausa da kuma irin gudummuwar da ta bada domin ci gaban al'umma.

Allah ya jikan jaruma A'isha Dan Kano da rahama, mu kuma idan namu lokacin yazo, Allah yasa mu cika da imani.

Saurari yadda ta kasance.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG