Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharhi Kan Fim Din Fuska Biyu


Umar kofar Mazugal

Umar kofar Mazugal wanda aka fi sani da Umar UK, ya ce sabon fim din sa Fuska Biyu fim ne da ya maida hankali dangane da matsalolin tsaro mussaman ma yawaitar garkuwa da mutane da ake yi a yanzu.

Ya ce ya zabi jigon fim din Fuska Biyu duba da yadda yawaitar garkuwa da mutane, matsalolin rashin tsaro da rikice-rikicen da ke faruwa sanadiyar rashin tsaro.

Ya kara da cewa fim din yayi duba kan tarbiya, makarantun da yara ya kamata su shiga, abokai da sauransu tare da fito da hanyoyin da idan iyaye suka bi za’a magance matsalar samun masu tada zaune tsaya a cikin al’umma

Ya ce sun fuskanci kalubale da dama mussaman ma a lunguna da suka yi ta zuwa domin daukar fim, tare da cewar har yanzu al’umma bata samu wayewar kai ba a lokacin da ake daukar aikin fim.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:57 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG