Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sergio Aguero ya jefa kwallon sa ta 100


Dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero ya jefa kwallon sa ta 100 ma kungiyar sa a gasar rukunin firimiya lig ta Ingila wadda ta yi kunnen doki da ci 1 - 1 da kungiyar Newcastle jiya talata a filin wasa na st. James Park.

Dan wasan dan kasar Argentina shi ya fara jefa kwallo a wasan na jiya a lokacin da Aleksander Kolarov ya bugo cikin raga. Bidiyon da aka sake nunawa na wannan kwallo ya nuna cewa yayi satar gida kafin ya jefa kwallon amma ba'a soke jefawar ba.

Dan wasan Newcastle Vurnon Anita ya ramawa kungiyar tasa wannan kwallo daga bisani.

Aguero shine dan wasa na uku wanda ba dan asalin nahiyar Turai bane ya jefa kwalllaye har 100 a gasar Firimiya Lig ta Ingila, Sauran biyun sune Diedier Drogba da Dwigth Yoke.

Haka kuma Aguero shine dan wasa na biyu da ya sami kaiwa ga jefa kwallaye 100 cikin mafi kankanci inda ya jefa kwallaye cikin wasani 147 da ya buga. Mutum daya dake gabansa shine gwanin tamaula Alan Shearer na Newcastle wanda ya jefa kwallaye 100 cikin wasanni 124.

Samakon wasan jiya dai ya tabbatar da Manchester City a matsayin ta uku a teburin Firimiya Lig, maki daya a gaban kungiyar Arsenal dake ta hudu wadda kuma gobe alhamis zata kara da west Brom.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG