Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aston Villa Ta Dakatar Da Agbonlahor Har Sai An Kammala Bincike


Aston Villa
Aston Villa

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Aston Villa, ta dakatar da Gabriel Agbonlahor, dan wasan gaba, biyo bayan rahoton zargi ta wata jarida ta wallafa cewa ya shaki hudar ibilis, a wajen wani biki da ya halarta a ranar da kungiyar sa ta Aston Villa, ta samu koma baya a gasar primiya lig.

Agbonlahor, dan shekaru 29, da abokansa sun halarci biki ne bayan da Manchester United, ta nakadawa Aston Villa kashi da ci daya da babu wanda yayi sanadiyar koma bayan da kungiyar ta Aston Villa, tayi.

Kungiyar tace ta dakatar da dan wasan ne wanda kuma shi yafi dadewa a klub din har sai an kamala bincike na cikin gida tu kunna.

Aston Villa, ta kara da cewa ba zata sake wani jawabi akan wannan batu ba har sai an kamala binciken da ake gudanarwa.

XS
SM
MD
LG