Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sepp Blatter Ya Ce Ya Kammala Aikin Sa


Bayan wani taro da manyan shugabannin hukumar kwallon kafa FIFA ta gudanar a birnin Zurich na kasar Switzerland, tsohon shugaban hukumar Sepp Blatter ya bayyana wa manema labarai cewar ya kammala aikinsa na kwallon kafa.

Ranar litinin din da ta gabata ne aka dakatar da Sepp Blatter da tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta turai UEFA Michel Platini daga yin duk wani aiki mai nasaba da kwallon kafa har na tsawon shekaru takwas a sakamakon zargin sa da biyan wasu makudan kudu har fan miliyan daya da dubu talatin da biyar da ba bisa ka’ida ba, wanda ake cigaba da bincike akai.

Platini ya bayyana cewar zai daukaka kara, a yayin da shikuma Blatter ya nuna alamun daukar kaddarar murabus a wata hira da yayi da mujallar Wall street.

A kalaman sa, tsohon shugabab ya bayyana cewa ya kamala aikinsa na kwallon kafa, kuma yace bashi da sauran kwarin gwiwa a wannan kungiyar tun daga ranar 27 ga watan Mayu da jami’an tsaron Amurka suka yi masa dirar maiki.

Daga karshe Blatter ya yi korafi mai yawa akan manyan kamfanonin da ke daukar dawainiyar wasan cin kofin duniya kamar su Coca-Cola, da Mc Donald’s Visa da sauran su da sukai barazanar zare hannuwansu.

Blatter yace akwai kamfanoni da dama da ke layi suna jiran a basu dama domin zuba jarin su.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG